Cikakken Bayanin Maryam Yahaya Akan Rashin Lafiyarta

Jarumar Kannywood wadda tauraronta ke haskawa wato Maryam Yahaya tayi cikakken bayani akan rashin lafiyar da tasha fama da ita.
Hakan ya farune a sakamakon jita-jita, kareraki, sharri da kuma kage da yan Social Media ke yima Maryam Yahaya dangane da rashin lafiya dake damunta.
Jarumar ta fito tayi magana kan gaskiyar abunda ke damunta bayan lokaci da ta dauka ba’aji daga bakinta ba inda mutane keta yi mata rade-radi na abubuwan sharri da yawa.
Maryam Yahaya ta shaidawa mutane cewa Typhoid da Malaria ne tasha fama dasu inda ta kwashe tsawon wata guda tana jiyya amma yanzu ta warke ta samu sauki ta samu lafiya.
Ta kuma karyata mutanen dake cewa aljannu ne suka shafeta da kuma masu cewa shifa ce.
Daga karshe dai muna mata fatan Allah ya kara bata lafiya da kuma daukacin musulmai baki daya Ameen.
Saurari cikakken bayanin jarumar daga bakinta a hirar da aka yi da ita daga kasa.












