MOVIE: Labarina Season 5 Episode 4 (Complete)

Bayan dogon hutun da akayi bisa tsayawa aikin wannan shahararren shirin mai dogon zango wato LABARINA saboda maye gurbin wasu jarumai da bazasu sake fitowa a wannan shiri ba.
A yanzu dai babu jarumi Nuhu Abdullahi wanda ake kira da suna “Mahmud” a cikin wannan shirin yayinda ita kuma Nafisa Abdullahi wadda ake kiranta da “Summaya” kwantaraginta ya kare.
An maye gurbin jaruma Nafisa Abdullahi (Sumayya) da Fati Washa wanda zata hau sunan Summaya inda kuma shi Nuhu Abdullahi (Mahmud) daman an riga da an kashe shi tun cikin zango na hudu wato season 4.
Labarina shiri ne mai dogon zango wanda shirin ya samu kyakyawan aiki daga kwararre kuma babban Director wato Malan Aminu Saira inda shirin ya samu karbuwa sosai a wajen mutane wanda tashar Arewa24 da kuma tashar YouTube mai suna Saira Movies ke haskawa a duk sati ranar juma’a da misalin karfe takwas na dare 8PM.
Zaku ga irin yadda za’a cigaba da fafatawa tsakanin Presido da kuma Lukman wajen takarar neman auren Sumayya wanda kuma akwai gwagwarmaya tsakanin Presido da Baba Rabe duba da shine mahaifin Sumayya saboda ya keta masa haddi yaci mutuncinsa a zaman da sukayi a gidan gyaran hali.
Kalli complete Labarina Season 5 Episode 4 daga kasa don ganin cigaban abunda zai faru a wannan satin.












