Entertainment

Duk Miji Yana Son Jin Wadannan Kalamai Daga Bakin Matarsa

Miji da Mata

Mata ga wasu kalamai da babu wani namijin da baya so yaji matarsa ta furta mata su sai dai namijin da bai san darajar soyayar aure ba.

Yana da kyau a kalla duk wata mace tayi kokarin furtawa mijinta akalla kalma guda daya duk rana.

Hakan yana da matukar tasirin da zai inganta Zamantakewar auren su.

Ga wadannan kalamai kamar haka:

1: Ban taɓa danasanin auren ka ba.

2: Nayi sa’ar samun miji.

3: Ina alfahari da kai.

4: Na yarda da kai 100 bisa 100 mijina

5: Na gode.

6: Allah Ya ƙara buɗi.

7: YI haƙuri.

8: Na tuba.

9: Ka ƙara hakuri dani

10: Ka sanar dani abubuwa da dama a rayuwata.

11: Da duk maza kamarka suke da mata sun huta.

12: Kalamanka kawai suke sani tsuma.

13: Ka shagwaɓani da soyayya

14: Ina godiya da irin ɗawaniyar da kake yi damu.

15: Soyyya da kaunar da kake nuna mini sune suka ɗaukaka matsayina

16: Ina murna idan naga ko naji ka kyautatawa wasu.

17: Dole ke sa nake nesa da kai.

18: Ina kara sonka a kowani daƙiƙa.

19: Kaine mutuncina.

20: Ko a Aljanna dakai nake burin rayuwa na har abada.

Da fatan zaku yi amfani da su ta hanyar data dace, da kuma lokacin daya dace.


Abubakarfcb

Abubakar Umar famously known as Abubakarfcb (FCB) is the Founder and CEO of BlogLoaded.Com. He is a Blogger, Content Creator, Freelancer, Microbiologist and Tech Enthusiast. Contact him directly by clicking on any of the social media buttons below.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button