News

Yadda Zakayi Rejistar Katin Zabe Da Wayarka Cikin Sauki

Katin Zabe (Voter’s Card)

Yanzu haka Hukumar Zabe ta Kasa wato INEC ta fara yin Rejistar Katin Zabe tun ranar 28 ga watan June na wannan shekarar ta 2021.

Hukumar ta bude wannan shafi na yanar gizo don samama yan Najeriya sauki gurin yin katin zabe ko sabunta shi ga wanda nashi ya bace ko ya lalace.

Yi Kokari ka Mallaki naka kuma kasanar duk wanda bashi da shi, shima ya mallaki nashi.

Kuyi Rejista Zabe domin Zabar Shugaba nagari.

Sai kaga mutum baya zabe amma yafi kowa zagin shuwagabanni.

Babu yadda za’ayi a samu gyara a Kasa, Jaha da Kananan Hukumomi har sai al’umma ta zabarwa kanta shugaba nagari.

Ba zaka zabi shugaba nagari ba, har sai kana da Katin Zabe, ko da kuwa waye kai a Kasarnan.

ABUBUWAN DA AKA AMINCE MUTUM YAYI A SHAFIN:

1. Sabuwar Rigista

2. Sabunta Katin daya Bata ko Lalacewa

3. Canza mazaba ko akwatin Zabe

4. Gyaran Suna ko Shekarun Haihuwa.

Abunda mutum ke bukata na dole a Ofishin Hukumar Zabe shine daukar zanen hannu ga mai sabuwar Rijista da kuma karbar Katin na Dundindin idan ya fito.

Danna wannan link na kasa domin yin sabuwar rejista ko sabuntawa.

https://cvr.inecnigeria.org/


Abubakarfcb

Abubakar Umar famously known as Abubakarfcb (FCB) is the Founder and CEO of BlogLoaded.Com. He is a Blogger, Content Creator, Freelancer, Microbiologist and Tech Enthusiast. Contact him directly by clicking on any of the social media buttons below.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button